Saturday, 12 January 2019

Shugaba Buhari ya cancanci yabo saboda cewa da yayi bazai yi amfani da kudin gwamnati ba wajan yakin neman zabe>>Sanata Shehu Sani

"Shugaba Muhammadu Buhari ya cancanci a yaba masa, kasantuwarsa shugaba na farko da ya fito ya ce ba zai taba aminta ba da yin amfani da dukiyar baitil malin kasa domin yakin neman zabe.


Sai gashi kuma wasu gwamnonin jihohin Nijeriya da wasu shugabannin manyan Ma'aikatun gwamnati suna kyautar daruruwan motoci domin yakin neman zabe.

Saboda haka nake kira gare su da su kula sosai wajen mikawa zaki nama, domin wata rana hannayensu zai cafke ya hada da naman ya cinye"

Kalaman Sanata Shehu Sani

Daga Real Sani Twoeffect Yawuri


No comments:

Post a Comment