Monday, 7 January 2019

Shugaba Buhari ya gana da dattawan jihar Borno: Gwamna Kashim Shattima ya fashe da kuka a gaban Buhari saboda koma bayan da aka samu a yaki da Boko Haram

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya gana da dattawan jihar Borno da suka hada da sarakunan gargajiya wanda gwamnan jihar, Kashim Shattima ya musu jagora.The Cable ta ruwaito cewa, dattawan na Borno sun jewa shugaba Buhari da kokon bararsu akan koma bayan da aka samu a yakin da ake yi da Boko Haram inda suka ce gwiwarsu ta yi sanyi.

A lokacin da yake jawabi ga shugaban kasa, Gwamna Kashim Shattima ya fashe da kuka bisa wannan koma baya da aka samu a rikicin na Boko Haram a jiharshi, The Cable ta ruwaito cewa saida aka bukaci 'yan Jaridar su bar dakin taron na wani lokaci bayan gwamna n ya fara zubar da hawaye.

Gwamnan ya shaidawa shugaba Buhari cewa basa tantamar shi akan cewa zai iya gamawa da Boko Haram dan haka suna bukatar daukin gwamnatin tarayya a jihar tasu.
No comments:

Post a Comment