Friday, 4 January 2019

Shugaba Buhari ya godewa A'isha bisa goyon bayan da take bashi

A jiyane shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da tawagar yakin neman zaben  mata da matasa da uwargidanshi,Hajiya A'isha Buhari ta shiryamai, a jiyandai A'isha ta yi inkiyarnan ta 4+4 wanda hoton ya watsu sosai a shafukan sada zumunta kamar wutar daji.Da alama abinda uwargidan nashi ta mai ya farantamai rai sosai domin kuwa shugaba Buharin ya fito ta shafinshi na sada zumunta inda ya ce, ina godemiki da goyon bayan da kike bani.

No comments:

Post a Comment