Friday, 4 January 2019

Shugaba Buhari ya kaddamar da tawagar yakin neman zabenshi ta mata da matasa saidai Tinubu da Oshiomhole basu halarta ba

Wadannan hotunan shugaban kasa, Muhamadu Buharine da matarshi, Hajiya A'isha tare da sauran wasu manyan mukarraban jam'iyyar APC a jiya, Alhamis a fadar shugaban ta Villa dake Abuja inda ya kaddamar da tawagar yakin neman zabenshi ta mata da matasa da A'ishar ta shirya mai.Saidai wani abu da ya dauki hankulan mutane lokacin wannan taron gangamin shine babu wasu jigogin jam'iyyar ta APC irin su shugabanta, Adams Oshiomhole da Bola Ahmad Tinubu a gurin.
No comments:

Post a Comment