Thursday, 24 January 2019

Shugaba Buhari ya sakawa dokar hana nunawa nakasassu kyama hannu: Akwai tarar Miliyan daya ga wanda ya karya wannan doka

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sanyawa dokar hana nunawa musakai kyama a cikin al'umma hannu, dokar ta bayar da dama ga musakai, misalin makafi, guragu, kurame da sauransu da suma su fara aikin gwamnati.A wata sanarwa da me baiwa shugaban kasar shawara akan harkokin majalisun tarayya, Sanata Ita Enang ya fitar ranar Larabar da ta gabata, anji cewa, a yanzu duk wanda aka samu da nuna kyama ga nakasassu zai fuskanci fushin hukuma.

Hukuncin dake kan kamfani da ya nuna kyama ga nakasassu shine tarar Naira Miliyan daya idan kuma mutumne zai biya Naira dubu Dari, ko kuma zaman gidan kaso na tsawon watanni 6.

Dokar ta bukaci kada a nunawa nakasasshe kyama a duk inda aka hadu dashi, a abin hawane, wajan aiki ne, dama dai duk inda ake samun taron jama'a.

Haka kuma dokar ta baiwa ma'aikatu na gwamnati da masu zaman kansu shekaru 5 da su canja tsarinsu yanza zasu samarwa nakasassu abubuwa na musamman da suka dace da yanayin da suke ciki.

Haka kuma ba'a yadda a yi ginin wata ma'aikata ba ba tare da samar da yanayi ko guri na musamman ba da zai dace da matsayin nakasassu ba.

Haka kuma dokar dai tace daga yanzu dolene duk wata ma'aikata ta rika warewa nakasassu kashi 5 cikin 100 na ma'aikatan da zata dauka aiki.

Sannan kuma dokar ta bayrda damar samar da ma'aikatar kula da nakasassu.

No comments:

Post a Comment