Monday, 7 January 2019

Shugaba Buhari Zai Gudanar Da Yakin Neman Zabe Ga Dukkanin 'Yan Takarar Jam'iyar APC

Biyo bayan tambayoyi da maganganu da ake ta yi a kafafen yada labarai akan ko shugaba Muhammadu Buhari zai yi yakin neman zabe ga jam'iyarsa ta APC da ma sauran 'yan takara na jam'iyar APC ne fadar shugaban kasa ta ga ya dace ta fito fili ta shaida wa jama'a cewar shugaba Muhammadu Buhari a matsayin sa na dan jam'iyyar APC kuma wanda zai tsaya takarar kujerar shugaban kasa a jam'iyyar tabbas zai gudanar da yakin neman zabe ga dukkanin 'yan takarar da jam'iyarsa ta tsayar a matakai daban-daban a zaben 2019.


Fadar shugaban kasa har wa yau a cikin rahotan da ta fitar ta ce, koda yake shugaba Buhari mutum ne da babu ko shakka yake da goyon bayan dimbin 'yan Nijeriya, wannan ba zai hana shi fita yakin neman zabe ba domin wannan shi kara ba shi damar lashe zaben da gagarumin rinjaye.

Sanarwar ta kara da cewar wannan ba wani abinda zai kawo rudani bane, domin shugaba Buhari shine jam'iyyar APC kuma ita ce shi.

Saboda haka shugaba Buhari zai yi yakin neman zabe ga kansa da sauran duk 'ya'yan jam'iyyar a bangarori daban-daban.


Daga Real Sani Twoeffect Yawuri

No comments:

Post a Comment