Wednesday, 23 January 2019

SIYASA BA DA GABA BA: Gwamna Tambuwal na Sakkawato ya karbi shugaba Buhari a filin jirgi

Gwamna Tambuwal ya karbi Shugaban Kasa, Muhammad Buhari a filin jirgin saman kasa da kasa na Sarkin Musulmi Abubakar Na Uku, a lokacin da ya isa jihar Sokoto domin yakin neman sake zaben shi karo na biyu a jihohin Sokoto da Kebbi, inda Shugaban kasa ya samu kyakkyawar tarbo ga dinbin mutanen da suka fito suna sai Baba, kafin ya wuce zuwa fadar mai Alfarma Sarkin Musulmi inda ya kai ziyara ta musammam. 


Rariya
No comments:

Post a Comment