Monday, 7 January 2019

Sojoji sun yi juyin mulki a kasar Gabon

Sojoji a kasar Gabon sun bayyana cewa sun yi juyin mulki bayan shekaru 50 iyalin shugaban kasar na rike da madafan iko.
BBC ta ruwaito cewa,sojojin sun bayyana juyin mulkin da cewa sun yi shine dan dawo da dimokradiyya kasar, sun kama iko da gidan rediyon kasar inda suka fitar da sanarwar juyin mulkin sannan kuma tankokin yaki sun bazu akan titunan babban birnin kasar, Libreville.

Ali Bongo ya gaji dan uwanshi Umar Bongo a shekarar 2009. Haka kuma ya sake lashe zabe a shekarar 2016 inda ya lashe zaben kasar da tazarar kuri'u kadan a zabe me cike da rudani.

Ya kwashe watanni 2 yana jiyya a kasar Morocco bayan ciwon shanyewar rabin jiki da ya sameshi.

Dan ya kawar da rade-radin dake yawo akan lafiyarshi shugaban ya mika sakon sabuwar shekara ta talabijin inda yace yana samun sauki, sakon da sojin suka bayyana a matsayin kokarin dagewa akan mulki ko ta halin kaka da shugaban ke yi.


Wani soja wanda shine shugaban wata kungiyar dake ikirarin kare tsaron kasar ta gabon, Lt Kelly Ondo Obiang ya bukaci matasa su tashi tsaye su kare kasarsu, ya kuma bayar da umarni ga sojoji da su kama iko ta harkar tafiye-tafiye da filayen jirgin sama da sauransu.

Babu wata sabarwa daga gwamnati zuwa yanzu.

No comments:

Post a Comment