Thursday, 24 January 2019

Taurarin fina-finan Hausa da suka shahara da bayar da taimako

Bayan da ya bayyana yanda Rahama Sadau ta dauki nauyin kai Sani Garba S.K Asibiti jiya, tauraron me bayar da umarnin fina-finan Hausa, Aminu S. Bono ya kuma lissafo taurarin fina-finan Hausa da ke taimakawa junansu a masana'antar ta Kannywood, Aminu ya bayyana cewa yayi wannan rubutune a matsayin raddin ga wasu da suka rika sukar  Kannywood akan dambarwar Chiroki.Ga abinda ya rubuta kamar haka:
TSAKANIN KANNYWOOD TA YAU DA KUMA TA JIYA 
Bismillahi wassalatu ala rasulullah

Da farko inaso mai karatu ya fahimci cewa wannan rubutu nawa nayishi ne domin wani abu daya faru akan maganar CIROKI 
dangane da yadda alumma sukai mirsisi gurin kin yiwa YAN KANNYWOOD adalci ,to Amma fa ina ganin laifin mune 
MENENE LAIFIN ?

E mana laifin shine duk lokacin da wani jarumi ko jaruma ko producer ko darakta yayi wani abun alheri sai muyi shiru Amma idan akasin haka ya faru sai magautan harkar na ciki da waje suyi ta kwarmato har abin ya kewaya gari .

TAIMAKO 
Shin bai halatta bane idan akai aikin alheri ayi shiru kada a bayyana 
ALI NUHU 
Wallahi bansan sau nawa ina tare dakai aka kawo maka labarin wane yashig matsala kuma ka taimakaba haka kawai kake neman mutum kabashi ko bai tambayeka ba wannan al,ada taka sai take birgeni har nake fatan Allah yasa nima na taimaki wani Dan masana,antar batare da ya tambayeniba shin Ali nuhu lokaci baiyiba kuwa na bayyana alherin da kakeyi don gudun butulci irin nasu mai saida KUNUN CAN 
IBRAHIM MANDAWARI 
Dattijo kuma mai unguwar mandawari Allah yaja daran mai unguwa na tabbata yayi zamani da mai KUNU kuma baifi shi samun kudiba a wancan lokacin Amma dayake shi mutum ne cikakke sai gashi yau a matakin mai unguwa yake cikin rufin asiri harma ace ana neman taimako kuma ya taimaka wannan shine ake cewa TANADIN GOBE A YAU 
ADAM ZANGO

Nasanshi sosai kamar yunwar cikina bansan sau nawa ya dakko tsoffin jarumai irinsu MAI KUNU don yin aiki dasuba musamman tarayyarsa da darakta falalu sune suka canja marigayi IBRO izuwa jarumin da zai tsaya da kafarsa ya kuma sanya farashi daidai da shahararsa cikin mutunci da mutunta juna na tabbata da MAI KUNU yabi tsarin MARIGAYI da bai zagi wadanda basu da hannu cikin yanayin daya shigaba 
HADIZA GABON 
Tunda nake bantaba ganin jaruma mai taimakonta ba bazan manta sanda kikaje gidan DAUDU GALADANCI ba da irin alherin da kikaje dashiba dukda sanda yayi wasan kwaikwayonsa bama a haifekiba bazan manta taimakon dakikaiwa abokanan aiki daban daban ba ciki hardani nasani bakwason a fada Amma hakuri zakuyi mufadi don bamajin dadin zaginku da akeyi bada hakkinkuba

No comments:

Post a Comment