Friday, 4 January 2019

Tsohon gwamnan Kano Hamza Abdullahi ya rasu

Tsohon gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, AVM Hamza Abdullahi mai ritaya, ya rasu.


Rahotanni sun ce Hamza Abdullahi ya rasu ne a wani asibitin kasar Jamus ranar Laraba.
Ya mutu ne yana da shekara 73 a duniya.

Marigayin ya zama gwamnan Kano ne daga shekarar 1984 zuwa 1985, lokacin da Janar Muhammadu Buhari ke shugabancin Najeriya.

AVM Hamza Abdullahi ya rike mukamai da dama, ciki har da ministan birnin tarayya Abuja.


BBChausa.

No comments:

Post a Comment