Wednesday, 9 January 2019

Wani dagaci a jihar Kebbi yayi amfani da kudin da gwamnatin jihar ta bashi ya sai mota ya samarwa da jama'ar yankinshi ruwan sha

Wani Dagaci a karamar hukumar mulki ta Yawuri dake Jihar Kebbi yayi amfani da tallafin Naira Dubu Dari Biyu (N200,000) da gwamnatin Jihar ta Kebbi ta baiwa dagatai domin sayen motar hawa ya gyara famfon bohol na unguwarsa domin jama'a su amfana 


Dagaci/hakimin yankin Nasarawa dake cikin karamar hukumar mulki ta Yawuri  Alhaji Lawali Abdullahi  Zubairu  ne ya gabatar da wannan aikin alherin ga al'ummar da yake  shugabanta domin tsamosu daga mawuyacin halin da suka shiga na rashin ruwan sha a yankin 

ita dai wannan rijiyar bohol da hakimin ya gyara an ginata ne tun a shekarar 2016 ba tareda tayi aiki ba domin samar da ruwan sha ga al'ummar yankin ba 

Hakimin yayi amfani ne da wani tallafin sayen motocin hawa da gwamnatin Jihar ta baiwa hakiman Jihar na Naira dubu dari biyu (N200,000) yayi wannan aikin Alheri.

Hakimin yayi hakan ne domin ya ceto jama'arsa daga matsalar ruwan sha maimakon sayen motar hawa a lokacin da al'ummarsa suke fama da masifar rashin ruwan sha. 

Muna addu'a Allah ya karo mana shugabanni masu kaunar cigaban talakawansu irinsa ya kuma biyashi da gidan aljanna, amin.

Daga Real Sani Twoeffect Yawuri


No comments:

Post a Comment