Thursday, 10 January 2019

Wani malamin addini ya bayyana cewa shugaba Buhari zai mutu kamin zabe

Me kare muradin gwamnatin shugaban kasa musamman a shafukan sada zumunta, Kayode Ogundamisi ya saka wani fasto daga kasar Afrika ta Kudu da yayi kintacen cewa shugaba Buhari ba zai kai lokacin zabe ba sannan ya mayarmai da martani.Fasto me suna Samuel Akinbodunse ya bayyana cewa, Allah ya gayamai shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba zai kai lokacin zabe ba, mutuwa zai yi.

Kayode yace, dan Allah menene sunan wannan faston?

zan so ace bayan kintacen mutuwar shugaba Buhari fastoci zasu rika kuma kintacen mutuwar shuwagabannin kungiyar Boko Haram, da alama Allahn da suke bautawa yana mancewa ne irin wadancan mutane.

No comments:

Post a Comment