Friday, 4 January 2019

Wani na tare da Atiku yace shi fa yana ganin ba zasu kai labari ba

A yayin da ake ci gaba da yakin neman zabe tsakanin 'yan takarar mukamai daban-daban da zasu fafata a zaben shekarar 2019 dinnan da muke ciki, wani magoyin bayan dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a zaben watau Atiku Abubakar, ya fito ya nuna karayarsa a fili.


Mutumin ya bayyana ta dandalinshi na sada zumunta cewa, gaskiya irin yakin neman zaben da Atiku ke yi ya ban kunya gani nake kamar ma mun yi rashin nasara.

Me baiwa shugaban kasa shawara ta fannin sabbin kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad ya bashi amsar cewa, Ayya, nasan irin yanda kake ji, na lura komai ya tabarbare muku, hadda tsare-tsaren da kuka je kuka yi a Dubai. Kun riga kunyi rashin nasara saboda 'yan Najeriya ba zasu koma baya ba, sun zabi su je mataki na gaba.

No comments:

Post a Comment