Thursday, 3 January 2019

Yadda Jama'a Suka Dinga Cincirindon Neman Samun Tabbarukin Sheik Dahiru Bauchi A Saudiyya

A jiya 02/01/2019 mutane daga sassan duniya daban daban suka yi ta cincirindon ziyarar neman tabarukki daga Maulana Shehu Dahiru Usman Bauchi RTA, a Masallacin Manzon Allah  SAW, bayan kamalla sallar Azahar.Jama'a da dama waɗanda mafiya yawansu ba ƴan ƙasar Najeriya bane sukai ta fizgowa da ɓuɓulowa don ziyaran Shehu duk da ba a faɗa musu ko shi wanene ba. Jama'a ba su gushe ba suna ta ɓuɓulowa har sai da hadiman Shehu suka gudu da Shehu saboda cikowan jama'a. 

Wannan al'amari yana nuna muna cewa, lallai waliyai a duk inda aka gansu akan tuna da Allah, domin hasken Annabi SAW ne yake tajalli a fuskokinsu. 

Allah ya bamu albarkan Shehu Amin.


No comments:

Post a Comment