Sunday, 13 January 2019

Yadda Shugaba Buhari da IBB suka koreni daga aikin soja>>Inji dan marigayi Shehu Shagari

A hirar da yayi da gidan jaridar The Sun, babban dan tsohon shugaban kasa, Marigayi Alhaji Usman Shehu Shagari, watau captin Bala Shagari ya bayar da labarin yanda shugaban kasa,Muhammadu Buhari da tsohon shugaban kasa, janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB suka tursasamai barin aiki bayan da akawa gwamnatin mahaifinshi juyin mulki.Bala yace, a lokacin da akawa maihaifin nashi juyin mulki yana aikin soja bayan da akawa mahaifinshi juyin mulki kawai sai yaga takardar kora daga aiki aka bayyana mishi cewa an mishi ritayar dole, a wancan lokacin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne shugaban kasa sannan kuma janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB ne shugaban soji, ya kuma bayyana mai cewa bisa ikon da aka bashi ya mai ritayar dole, ba'a bukatar aikinshi.

Bala ya kara da cewa nan take aka kamashi aka tafi dashi Kaduna ya kwana a hannun  hukumar 'yansandan farin kaya a tsare sannan daga baya akamai daurin talala a cikin gida na tsawon sati shida.

Da aka tambayeshi ko an gayamai laifin da yayi aka koreshi?

Sai yace a'a laifinshi kawai shine shi dan Shugaban kasar da aka wa juyin mulkine kuma suna kallonshi a matsayin barazana idan suka barshi ya ci gaba da aikin soja.


No comments:

Post a Comment