Thursday, 10 January 2019

'Yan Najeriya suna zargin Buhari a kan raguwar kudin Dangote

Hamshakin dan kasuwar nan a Najeriya Aliko Dangote har yanzu shi ne wanda ya fi kowa kudi a Afirika amma yawan kudin nasa sun ragu.


Mujallar Forbes ta wannan shekarar ta wallafa cewa har yanzu sunan Dangote ne a farko a jerin masu kudin Afirika da dala biliyan 10.3.

Wannan na nuna cewa kudin nasa sun ragu da kusan dala biliyan 2.


Mujallar Forbes din ta nuna cewa matsalar kasuwa ce da kamfanin siminti na Dangote ya fuskanta ya jawo raguwar kudin.

Mike Adenuga, shugaban kamfanin sadarwa na Globacom shi ne yazo na biyu a jerin sunayen masu kudin da kusan dala biliyan 9.2.

A bara dai jimlar kudin Mike din dala biliyan 5.3 ne.

Da dama masu sharhi a shafukan sada zumunta musamman Twitter suna dora laifin raguwar kudin Aliko Dangote a kan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment