Thursday, 10 January 2019

'Yan sanda na neman Ronaldo dan daukar gwayoyin halittarshi a ga ko sun yi daidai da wanda aka samu a jikin rigar matar da tace ya mata fyade?

Yanzu haka dai a can birnin Las Vegas na kasar Amurka 'yan sanda sun samun izinin daukar kwayoyin halittar tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal, Cristiano Ronaldo da ake kira da DNA dan gwada su a ga sun yi daidai da wanda aka samu a jikin rigar matarnan da ta yi ikirarin cewa ya mata fyade.An dai samu kwayoyin halittar ne a jikin rigar matar me suna, Kathryn Mayorga wadda take sanye da ita lokacin da ta yi ikirarin cewar ya mata fyaden, dan haka 'yansandan suka samu izinin neman kwayoyin halittar Ronaldo dan aga ko sun yi daidai da wanda aka samu a jikin rigar.

Dama dai rigar na ajiye a cikin akwatin bincike akan fyaden wanda Kathryn Mayorga ta zargi Ronaldo da yi mata a shekarar 2009.

Yanzu dai 'yan sandan na Las Vegas sun aikewa da 'yansandan kasar Italiya da bukatar samo kwayoyin halittar Ronaldon, kamar yanda Wallstreet journal ta ruwaito.

Kuma wasu na kusa da Ronaldon sun tabbatar da cewa dan kwallon zai bada hadin kai wajan daukar kwayoyin halittar nashi dan a kammala bincike.

Shidai Ronaldo ya sha musanta wannan zargi na fyade da Kathryn Mayorga take masa inda yace tana so ta bata mai sunane kawai.

No comments:

Post a Comment