Saturday, 12 January 2019

Yanda Gwamnatin APC ta bani cin hanci dan kar in koma PDP>>Gwamna Tambuwal

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da labarin yanda gwamnatin APC ta yi kokarin bashi cin hanci dan kada ya fita daga jam'iyyar.Gwamnan ya bayyana hakane a yayin da yaje yakin neman zabe a garin Silame dake jihar Sakkwato.

Yace a yayin da gwamnatin APC ta ji cewa zai koma PDP sai ta yi sauri ta bayar da aikin gyaran titin garin da ya fito dan ta ja ra'ayinshi ya tsaya a jam'iyyar, saidai Tambuwal yace sun makaro dan kuwa hakan bai sashi canja shawara ba.

Ya kara da cewa yunwar da ake fama da ita sanadiyyar rashin sanin makamar aiki ne na gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Yace APC ta yi watsi da mutanen ta dan haka su a sakkwato PDP zasu yi kuma zasu koyawa APC din darasi bisa tsanar da take nunawa mutane.

No comments:

Post a Comment