Friday, 11 January 2019

'Yansanda rufe da fuskoki sun tafi da sanata Dino Melaye kalli inda suka ajiyeshi

Da yammacin yaune labari ya watsu cewa wasu jami'an 'yansanda cikin badda kama sun shiga cikin asibitin 'yansanda da sanata Dino Melaye ke kwance suka daukeshi da karfin tsiya suka tafi dashi.'Yansandan sun zone da wata mota wadda itama ba'a ganin cikinta kamar yanda rahotanni suka bayyana.

Daga baya kuma sai wannan hoton ya bayyana a shafukan sada zumunta inda rahotanni suka bayyana cewa sanata Dino Melaye ne a kwance a kasa a ofishin hukumar 'yansandan farin kaya.

Ana dai zargin sanata Melaye da hannu a yunkurin kashe jami'in dan sanda.

No comments:

Post a Comment