Tuesday, 8 January 2019

Zanga-Zanga za mu fara ba yajin aiki ba>>NLC

Kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya ta ce za ta tsunduma zanga-zanga a yau, Talata kan yadda gwamnatin kasar ta gaza cimma matsaya kan mafi karancin albashin ma’aikata amma hakan baya nufin umartar daukacin ma'aikatan kasar su tafi yajin aiki.Babban sakataren NLC Dr Peter Ozo-Eson ya tabbatarwa kamfanin dillacin labaran kasar cewa matakin da za su fara dauka daga goben ba wai yajin aiki ba ne kamar yadda suka yi a baya, yana mai cewa zanga-zanga ce da za ta gudana a ilahirin sassan kasar.

Kungiyar kwadagon ta NLC dai ta tsaya kan bakanta wajen ganin lallai gwamnatocin kasar sun amince da Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikata sabanin Naira dubu 18 da su ke karba a halin yanzu.

Tun a ranar 17 ga watan Disamban bara, NLC ta sha alwashin maukar Fadar shugaban kasa ta gaza mika kudirin Karin albashin gaban majalisar don zamowa doka kafin 31 ga watan, babu shakka za ta dauki mataki na kashin kanta.

Yanzu haka dai Gwamnatocin jihohin kasar sun tsaya sun amince da kara mafi karancin albashin ma'aikatan zuwa Naira dubu 22 matakin da kungiyoyin kwadagon Najeriyar suka yi watsi da shi.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment