Tuesday, 12 February 2019

A karo na 3 gobara ta cinye kayan INEC


A karo na uku kusan a jere-a-jere an samu konewar kayan hukumar zabe me zaman kanta ta kasa, INEC, gobarar ta yau ta farune a jihar Anambra wadda ta yi sanadiyyar konewar kimanin sama da na'urar tantancewa 4000.

A baya dai an samu konewar ofisoshin hukumar INEC din a jihohin Abia da Flato.

Hukumar ta bayyana cewa wannan konewar kayan zaben bazai sa a dakatar da gudanar da zabe a jihar Anambran ba kamar yanda aka shirya da fari, za'a kawo kayan da suka yi rara na sauran jihohi dan yin amfani dasu a jihar.

No comments:

Post a Comment