Saturday, 16 February 2019

A wajan daukar fim na hadu da matata>>Ali Nuhu

Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu Sarki ya bayyana yanda ya hadu da matarshi, Maimuna a shekarar 2000. Alin yace ya hadu da matar tashine a lokacin da suke daukar fim din Wasila.


Ya bayyana cewa suna cikin daukar fim dinne sai ya ganta ta gitta, yana ganinta ya gayawa abokin aikinshi, Ishaq Sidi Ishaq da Hajara Usman cewa shi fa ya ga matar aure, kamar yanda ya bayyanawa Daily Trust a hirar da suka yi dashi.

Ali Da matarshi suna da 'ya'ya biyu mace da namiji,watau Fatima da Ahmad.

No comments:

Post a Comment