Sunday, 17 February 2019

Abubuwa biyar game da Najeriya: Shin kasar ta zama babbar kwabo a Afirka?

Sama da 'yan Najeriya miliyan 84 ne suka yi rajistar zabe, amma me kuka sani game da kasar da ta fi yawan mutane da karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka?


1) Kidan Afrobeats- Abinda kasar ta fi fitarwa

Kade-kaden Najeriya suna zagaye duniya inda suke samun karramawa a sassan duniya daban-daban.


Wannan kida na Afrobeat shi ne wanda marigayi Fela Kuti ya shahara da shi a tsakanin shekarun 1970 zuwa 1980.

Sabbin taurari a masana'antar kade-kade a kasar irin su Wizkid da Davido da Tiwa Savage da Jidenna sun zama mawakan da aka fi fitar da wakokinsu, wanda hakan ya jawo manyan kamfanonin kade-kade na duniya kamar su Universal Music Group da kuma Sony suka kafa ofisoshinsu a Najeriyar.

Bidiyon wakar Davido ta 'Davido's Fall,' wadda aka fitar a 2017 ita ce wakar da bidiyon ta ya fi shahara cikin bidiyoyin mawakan Najeriya da kusan mutane miliyan 100 suka kalla a shafin Youtube.

Wannan kidan na Afrobeats ba wai ya tsaya ba ne a nahiyar Afirka, ya zagaye kulob-kulob na duniya.

Kidan dai ya fara ne daga rukunin wakokin Najeriya da Ghana da suka kunshi nau'in wakoki irin su hiplife da azonto da kuma dancehell, sa'annan wakar D'banj ta 'Oliver Twist' ce ta fito da kidan afrobeats a 2012.

Sauran mawakan da suke bada gudummawa wajen habakar kidan afrobeats su ne Yemi Alade da Tekno da irin su Falz sai Olamide da Mista Eazi da kuma Mologo sai kuma Patoranking.

Daya daga cikin dalilin da yasa wannan kidan ya shahara shi ne kafiya irin na kidan.

2) Shahararrun marubuta
Ba wai a bangaren wakoki kadai Najeriya ta shahara ba, tana tinkaho da marubuta da suka shahara a kasar.

Wadanda suka fi shahara sune irin su Chinua Achebe wanda littafinsa mai suna ''Things Fall Apart'' ya zama littafin adabi da aka sayar da kusan guda miliyan 20 tun bayan wallafa shi a 1958.

Hakazalika an fassara littafin a harsuna 57.

A bangare guda kuma Wole Soyinka ya zama dan nahiyar Afirka na farko da ya taba lashe kyautar Nobel a bangaren adabi a 1986.

Sai kuma marubuta na yanzu kamar irin su Chigozie Obioma da Helon Habila sai Chibundu Onuzo su ma suna samun kyauttutuka saboda gudummawar da suke bayar wa wajen rubuce-rubuce.

Nwaubani ta shaidawa BBC cewa '''yan Najeriya suna so a gan su ko kuma a ji su.

Akwai daruruwan 'yan nahiyar Afirka da suke bayar da labarai masu dadi amma an fi kallon 'yan Najeriya saboda kwar jinin da suke da shi.

Ta kuma kara bayyana cewa "muna so mu zama a sama ko ta wane bangare. Muna so kowa ya sani idan mun shigo.''

Ganin cewa akwai karin maganar da ke cewa akwai hannun 'yan Najeriya a kowace sabga, ba abin mamaki ba ne idan suna bayar da irin wadannan labarai masu jan hankali.

3) Shirin zarce Amurka

Mutum na cikin hatsari a Najeriya idan yana kokarin sanin wace kabila ko bangaren addini ne suka fi yawa a daidai lokacin da kasar take fama da rikice-rikice da kuma yawan san kudi ganin cewa ana duba yawan mutanen jiha wurin ba ta kasafin kudi.

Amma ba a musanta cewa yawan mutanen Najeriyar na karuwa sossai.

Nan da shekarar 2047, Najeriya za ta zarce Amurka wurin yawan mutane domin zama kasa ta uku da ta fi kowacce yawa a duniya da kusan mutane miliyan 387 kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashe.

Najeriya, matashiyar kasa da ke da yara 'yan kasa da shekara 14, kusan kashi 40 kenan cikin 100 na mutum miliyan 196.

Kuma ana sa ran kananan yara za su taka muhimmiyar rawa a wannan zabe da kusan rabin masu zaben 'yan kasa da shekara 15 ne.

Matasa wadanda suka gama jami'a suna yawan korafin cewa babu inganttatun ayyukan da za su yi kuma da yawansu suna tunanin barin kasar.

Ganin yadda yawan mutane ke kara karuwa a nahiyar Afirka, Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi gargadin cewa idan babu wani kyakkyawan shiri za a iya fuskantar matsala a nan gaba.

4) Yawan man fetur da karancin wutar lantarki
'Yan Najeriya da dama suna musun cewa kidan da ya fi tashe a kasar shi ne kidan Afrobeats, inda suke cewa karar janareto ne kidan da ya fi shahara.

Ko da a ce akwai wutar lantarki, ya zama dole su dogara a kan janarato sakamakon rashin tabbas na daukewar wuta.

Wasu wuraren suna shafe makwanni ba tare da wutar lantarki ba.

Duk da haka Najeriya ce kasar da ta fi kowace kasa samar da man fetur a nahiyar Afirka wadda kuma take samar da kusan ganga miliyan 2 ta man fetur.

Harajin da gwamnatin kasar take samu daga kamfanonin man fetur da kuma kudaden da take samu na kasashen waje ta hanyar fitar da man yana taka muhimmiyar rawa ga tattalin arzikin kasar.

Amma wasu 'yan kasar za su yi wuf su tuna cewa an barnatar da wadannan kudaden a shekarun da suka gabata.

5) Daular Boko Haram

Maudu'in #BringBackOurGirls wanda maudu'i ne na kungiyar nan mai fafutukar ganin cewa an ceto 'yan matan Chibok ya ja hankalin duniya musamman a kan ta'addanci irin na kungiyar Boko Haram.

Garkuwar da 'yan kungiyar suka yi da 'yan matan a 2014 ya fito da akidar kungiyar karara ta kiyayya ga karatun boko.

An kirkiro kungiyar Boko Haram ne a 2002 a birnin Maiduguri dake arewa maso gabashin Najeriya, inda mazauna wannan yankin suka lakaba wa kungiyar suna Boko Haram.

A tarihi, Sarakunan arewacin Najeriya sun ki amince wa da salon mulkin mallaka na kai-tsaye wato indirect rule.

Amma Andrew Walker mawallafin littafin nan mai magana a kan Boko Haram mai suna "Eat the Heart of the Infidel," ya ce wannan akidar ta yi zurfin da ya wuce tunani.

Mista Andrew ya shaida wa BBC cewa ''akwai tarihi mai tsawo a kan yadda aka ki amince wa da karatun Boko a arewacin Najeriya saboda karfin Musulunci a wannan lokaci.''

Amma a shekaru hudu da suka wuce, rundunar sojin kasar tare da tallafin kasashen ketare sun taimaka wajen kwato wasu garuruwa da kungiyar take da iko da su a da da kuma kwato mutane da dama da aka yi garkuwa da su.

Amma duk da haka, 'yan tayar da kayar bayan suna ci gaba da kai hare-hare a wasu sassa, ganin cewa kungiyar a yanzu ta rabu, inda har wani bangare ke goyon bayan kungiyar ISIS.

Har yanzu dai akwai sauran 'yan matan Chibok kusan 112 da ke hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram.
BBCHausa.

No comments:

Post a Comment