Thursday, 7 February 2019

Adam A. Zango ya koma Bayan Atiku

Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango wanda a da yana gaba-gaba wajan goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood yanzu dai ya canja sheka zuwa PDP har ma ya hadu da Atiku ya kuma bayyana goyon bayanshi a gareshi.Adam A. Zango ya bayyana cewa, bai taba tsammanin haka Atikun ke da haba-haba da mutane ba sai da ya hadu dashi.

Ya kuma ce ita kanta APC din tana nufin Atikune.

Masoyan Adamun da dama sun bayyana ra'ayoyinsu a shafukan sada zumunta wanda ta kaiga sai da ya rufe bayar da damar bayyana ra'ayoyi akan al'amuran shafinshi watau Comment na Instagram.

Ga abinda wasu suka bayyana akan hakan:

No comments:

Post a Comment