Sunday, 17 February 2019

A'isha Buhari ta yi murnar cika shekaru 48

Uwar gidan shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari ta yi murnar cika shekaru 48 a Duniya, an haifi Hajiya A'isha a ranar 17 ga watan Febrairun shekarar 1971.An daura mata aure da shugaba Buhari a ranar 2 ga watan Disambar shekarar 1989, suna da 'ya'ya biyar tare.

Ta yi karatun digiri na farko a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria akan public administration sannan ta yi digiri na biyu akan dangantakar kasashen Duniya daga jami'ar soji ta Kaduna.

Muna tayata murna da fatan Allah ya karo shekaru masu Albarka.

No comments:

Post a Comment