Tuesday, 12 February 2019

Akwai Malamai Magada Annabawa, Akwai Kuma Malamai Magada Dalar Amurka>>Sanata Kwankwaso

MALAMAI FA SUN KASU KASHI-KASHI

A wata hira ta musamman da aka yi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso akan maganganun da ya fadi akan wasu Malamai ga abinda ya jaddada kamar haka:


"Mu muke girmama Malamai, Malamai iyaye ne, kuma muna gaya musu su daina shiga harkar siyasan mu, in ba zasu zabe mu ba kar su aibata mu, Malamai irin su Malam Abba Koki, Malam Nazifi, Dr Sani umar Rijiyar Lemo, Malam Sani Fagge, Mal Aminu Daurawa da sauransu ai sune Malamai, kuma Malamai sun kasu kashi gida biyu: Malamai magada Annabawa da Malamai Magada dalar Amurka..", inji Sanata Kwankwaso.
Rariya.


No comments:

Post a Comment