Monday, 18 February 2019

ALJANI NA IYA SADUWA DA JINSIN DAN ADAM>>Dr Ahmad Ibrahim BUK

A safiyar yau na saurari karatun Dakta Ahmad Ibrahim BUK akan Aljanu. A cewarsa, "Allah Ya halacci aljanu ta yadda zasu iya siffantuwa da wasu siffofi halittun. Su kan iya zama Mace ko Namiji su kuma kwashi kamanni da siffofin Dan Adam. 


Sai dai a yayin da suka rikida zuwa wata halittar mai rai, Dan Adam zai iya kama su, zai iya cutar da su zai iya kuma kashe su. Wannan ya sa da sun rikida zuwa wata halittar sai su yi sauri su koma asalin halittar su.

Sannan wani aljanin ya fi wani karfi, kamar yadda yanayin halittar Dan Adam ya ke. 

Domin karin haske na kira Dakta Ahmad a waya, na kuma tambaye shi akan shin Aljanu na iya saduwa da jinsin Dan Adam?

"Suna iya wa, Aljana tana iya saduwa da Namijin Mutum,  kamar yadda Aljani ya kan iya saduwa da Macen mutum. Mafi akasarin mafarkin jima'i da muke yi da aljanu muke tarawa. Wannan ya sa yanayin zakin jima'in ya ke bambanta da na jinsin Dan Adam."

Yaya Kuma batun Aljani ya yi wa Macen Mutum ciki ta haihu? Malam ya ce wannan akwai matsala domin kai-tsaye ba za ka iya ba wa mutum amsa ba. Yana bukatar zurfafa ilimi. Misali mace za ta iya zuwa ta yi zina ta dauki ciki, ta zo ta ce Aljani ne yayi mata. Waye zai yarda da ita? 

Akwai abubuwa da dama da ya kamata na tambayi Malam, amma kasancewar kada na dauke masa lokaci a matsayinsa na masu hulda da jama'a na saurara. 

Allah Ya karawa Malam Lafiya Da Nisan Kwana.
Maje El-Hajeej Hotoro.


No comments:

Post a Comment