Sunday, 17 February 2019

An gano 'ya mai shekaru dubu 5

A wasu tone-tone da masana tarihin al'umomin zaman dauri suka yi a arewacin kasar Iran,an gano kwarangwal na wata 'ya mace mai akalla shekaru dubu 5.


A cewar kafar yada labarai ta daliban Iran ISNA,wasu masanan tarihin kasar Farisa ne suka gano wannan jinjirar a jihar Mazenderan.

Shugaban wannan tawagar masana mai tone-tonen kasa,Muhammad Fazli ya ce,"A bincike-binciken da muka gudanar a garin Babol na yankin Mazenderan ne muka gano yarinyar mai kimanin 13 zuwa 14 a lokacin da ta kwanta dama. Yarinyar wacce cinkon wuri da na duwatsartsu ke rataye a wuyarka ta share shekaru dubu 5 a kushewarta gabanin masanan su tono ta".

Fazli wanda ya ce duk da cewa kawo yanzu mabinnatan gawarwaki na yankin na gina kaburruka ba tare da izini ba,wanda hakan na wahalar da su matuka gaya,amma ana ci gaba da gudanar da aiyukan tone-tone a yankin na Mazenderan.

A kasar Iran an fara gudanar tone-tonen gano kayayyaki tari na farko a shekarar 1850 a yankin Susa, a karkashin jagorancin Turawa.Tun a wannan zamanin,Iran ta ke ci gaba da bai wa izinin gudanar da bincike-binciken ga masanan kasar Faransa.

A shekarar 1937, a karo na farko masanan jami'o'in Tehran na kasar Iran suka kaddamar aiyukan tone-tone tare da hadin gwiwar gidan ajje kayayyakin tarihi na Bastan.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment