Friday, 15 February 2019

An samar da maganin dake warkar da cutar Kanjamau da kaso 90

Malaman Kimiyya a kasar Italiya sun samar da wata allurar dake maganin cutar Kanjamau da cuta mai karya garkuwar jiki take janyo wa da kaso 90.


Cibiyar Lafiya ta Kasa ta Italiya ta ce, Ma'aikatar Cibiyar Yaki da Kanjamau ne suka gudanar da aiyuka don samar da maganin cutar da cuta mai karya garkuwar jiki take janyo wa.

An buga sakamakon rahoton a mujallar Frontiers in Immonology inda aka bayyana ganin raguwar karfinta sosai ga mutanen da aka yi gwajin allurar a kansu.

An gwada allurar a kan mutane 90 ga aka sanya wa idanu tsawon shekaru 8.

Sakamakon binciken da Barbara Ensoli da abokanta suka ya bayyana bayan shekaru 8 karfin cutar ta Kanjamau ya ragu da kaso 90 cikin dari.

Tsawon shekaru 10 Ensoli da abokan aikinta suna bincike game da gano maganin cutar


No comments:

Post a Comment