Monday, 11 February 2019

An yiwa shugaba Buhari ruwan duwatsu a Ogun

A yayin yakin neman zaben da shugaban kasa, Muhammadu Buhari yaje yi jihar Ogun an samu wata 'yar hatsaniya da tasa aka jefeshi tare da shugaban jam'iyyar,Adams Oshimhole.Lamarin dai ya aukune a yayin da shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole ya hau dandamali zai fara jawabi, daga nanne sai aka samu wasu suka fara jifar shi da robar ruwa hadda dutsen, rahotanni daga Punch da Thisday sun tabbatar da cewa daya daga cikin duwatsun da aka jefo yayi kan shugaban kasa, Muhammadu Buhari dake zaune saidai daya daga cikin masu tsaron lafiyarshi ya tare dutsen be isa ga shugaban ba.

Hakan na faruwa sai jami'an tsaro suka kewa shugaba Buharin da mataimakinshi, Farfesa Yemi Osinbajo.

Rahotannin sun nuna cewa hakan ya farune sanadiyyar 'yan takarar gwamna biyu da ake cece-kuce akan su a jihar wanda kowane ke ikirarin cewa shine dan takarar jam'iyya, wannan lamari ya sa Uban jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu yin jifa da tutar APC sannan ya fice daga gurin taron cikin fushi yayin da shugaba Buhari ke yin jawabi.

A jawabinshi, shugaba Buhari ya bukaci jama'ar jihar da su zabi shugaban kasa na APC amma a matakin gwamna su zabi wanda suke so.

Kamin wannan lamari saida gwamnan jihar, Ibikunle Amosun amosun ya roki jama'ar da suka taru a gurin da kada su kunyatashi a gaban shugaban kasa.

No comments:

Post a Comment