Tuesday, 12 February 2019

Anya Chelsea za ta iya hakuri da salon horarwar Sarri?

Masu bibiyar wasanni na tafka muhawara kan makomar kocin Chelsea Maurizio Sarri a kungiyar, biyo bayan ruwan kwallaye 6 a ragarsu da Manchester City ta yi.Kayen da Chelsea ta sha ranar Lahadi a hannun City, shi ne mafi muni da taba gani a gasar Premier cikin shekaru 28, wato tun daga shekarar 1991.

Rashin nasarar Chelsea ta zo ne kwanaki 11 kacal, bayanda kungiyar Bournemouth ta lallasa su da kwallaye 4-0.

Kocin Chelsea Maurizio Sarri na fuskantar barazanar rasa aikinsa ne, la’akari da cewa mai kungiyar ta Chelsea, kuma attajirin Rasha, Roman Abramovich da ya saye ta a 2003, ba shi da hakurin jure fuskantar shan kaye, koda kuwa mai horarwa bai dade da soma aiki ba.

Idan za’a iya tunawa dai, ko tsaffin masu horar da Chelsea da suka ci wa kungiyar manyan Kofuna, wato Jose Mourinho, Carlo Ancelotti da Antonio Conte ba su tsira daga kora ba a karkashin shugabancin Abramovich, ballantana Sarri da ya shafe watanni 8 kadai daga cikin yarjejeniyar shekaru 3.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment