Friday, 22 February 2019

APC ta bayyana abinda zai faru idan Buhari ya fadi zabe

Mataimakin daractan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Waziri Bulama ya bayyana cewa idan shugaban kasar ya fadi zaben da za'a yi gobe, Asabar zai kira wanda ya lashe zaben ya tayashi murna.Bulama ya gayawa maneman labarai hakane jiya, Alhamis a babban birnin tarayya, Abuja.

Yace idan shugaba Buhari yaci zabe, wanda kuma dukkanin alamu na nuna hakan ne zai kasance, to zai godewa 'yan Najeriya sannan ba zasu yi wani gagarumin bikin murna ba saboda wani nauyi ne aka sake dorawa shugaban kasar kuma zai yi iya kokarinshi wajan ganin yayi abinda yafi na mulkinshi na farko.

Ya kara da cewa idan kuwa shugaban ya fadi zabe, muddin zaben an yishine bisa gaskiya babbu magudi to zai kira wanda ya lashe zaben ya tayashi murna.

No comments:

Post a Comment