Wednesday, 27 February 2019

Atiku bazai kira Buhari ya tayashi murna ba: Fashi ne aka mana da rana tsaka kuma kara zamu kai kotu>>PDP

Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar bazai kira Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya tayashi murna ba, kuma ta bayyana zaben da cewa fashine aka mata da rana tsaka.Jaridar The Cable ta ruwaito daya daga jigo a tafiyar Atikun kuma tsohon me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar shari'a, Kanu Agabi yana cewa tuni har sun hada kwamitin lauyoyi da zai shigar da kara akan zaben.

Yace sun bukaci a bashi kididdigar na'urar tantance katin zaben da aka yi amfani da ita a jihohin Borno, Yobe da Nasarawa amma har yanzu ba'a bataba.

No comments:

Post a Comment