Tuesday, 26 February 2019

Atiku ya doke Buhari a jihohin Plateau,Cross Rivers, Akwa-Ibom, Delta da Bayelsa

Dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Plateau inda ya samu kuri'u 548,665 shi kuwa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na APC ya samu 468,555.Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya lashe Cross River da kuri'a 295,737 inda ya kada Buhari na APC da ya samu kuri'a 117,307.

Dan takarar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya lashe jihar Akwa Ibom da kuri'a 395.832, yayin da abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC shugaba buhari ya samu kuri'a 175,429.

Dan takarar PDP Atiku Abubakar ya doke Buhari a jihar Delta.

Atiku ya samu kuri'a 594,068 yayin da Buhari ya samu kuri'a 229,294.

Atiku Abubakar na PDP ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Bayelsa.

Atiku ya samu kuri'a 197,933 yayin da ya doke shugaba Buhari na APC wanda ya samu kuri'a 118,821
BBChausa.

No comments:

Post a Comment