Tuesday, 26 February 2019

Atiku ya kada Buhari da tazara kadan a jihar Benue

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP,Atiku Abubakar ya kayar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC a zaben jihar Benue da tazarar kuri'u kadan.
Me karba da bayyana sakamakon jihar, Prof. Sabastine Maimako ya bayyna cewa dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya samu kuri'u 355,255, yayin da shi kuma shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tashi da kuri'u 347,668. Hakan na nufin Atiku yayi nasara akanshi da kuri'u 7,587 kenan, kamar yanda Punch ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment