Tuesday, 26 February 2019

Atiku ya kada Buhari a jihar Anambra inda mataimakinshi ya fito

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar yayi nasara akan shugaban kasa, Muhammadu Buhari a jihar Anambra da tazara me yawa, Jihar Anambrar dai itace jihar da mataimakinshi, Peter Obi ya fito.Prof. Francis Otunta ne ya amshi sakamakon jihar ta Anambra sannan ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakarne ke kan gaba a jihar da kuri'u 524, 738, yayin da shi kuma shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya samu kuri'u 33, 298.

Saidai ministan kwadago, Dr Chris Ngige wanda shine wakilin APC a jihar wajan zabe yayi watsi da sakamakon inda ya bayyana cewa akwai kananan hukumomin da aka samu rikici amma duk da haka aka saka sakamakonsu. 

No comments:

Post a Comment