Monday, 18 February 2019

Ba ni da sha'awar malamai da kungiyoyin addini su shiga harkar siyasa>>Inji Sheikh Sani Ashir Kano

Ba ni da ra'ayin Manyan Malamai da Kungiyoyi su shiga siyasa, wallahi ba ni da sha'awar su shiga siyasa, ni a sha'awa ta, su zama su ne alkalai.


Shuwagabannin Malamai, suna da izinin su kira kowane irin mutum. Da ace Malamai ba su da ra'ayin siyasa, idan suka kira kowane irin dan siyasa zai je, zai je zai saurare su (da nufin nasiha ko wata maslaha).

To amma saboda malamai sun cakuda, su ma sun shiga siyasa, yanzu zai yi wahala su kira wani wanda yake siyasa su ba shi shawara ko wani abu, sai ya fahimci cewa kawai kiyayya ce.

Ni tuni ina da wannan ra'ayin, kuma saboda abunda na karanta, wato a cikin littattafan malamai da suka rubuto akan siyasa.

Wannan ya sa ni ba ni da sha'awar babban mutum, da babban Malami, da kuma kungiyoyi su shiga cikin harkar siyasa.

Ni a wuri na aje mu je mu yi ta yin Da'awah, saboda ita siyasa matsalarta, duk Allah na iya jarrabarka da abunda kake so da wanda ba ka so, tana iya yiyuwa wanda kake so ya ci zabe, tana yiyuwa wanda ba ka so ya ci zabe, kuma idan ya ci zabe, yana iya daukar matakai iri daban daban.

Maimakon kungiyoyin addini su shiga siyasa musiba ta karu, gara su hakura, su zauna su cigaba da Da'awa da karantar da mutane. Inji Shehin Malamin, Dr. Muhammad Sani Ashir Kano

Allah ya sa mu dace.
Sarauniya.


No comments:

Post a Comment