Sunday, 17 February 2019

Ba siyasa ba ce ta sa muka dage zaben Najeriya>>INEC

Shugaban Hukumar Zaben Najeriya, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa, babu siyasa a batun dage zagen shugabancin kasar da na ‘yan majalisu zuwa makon gobe.
Farfesa Yakubu ya bayyana haka ne a taron manema labarai a birnin Abuja, in da yake cewa, dage zagen bai shafi batutuwan tsaro ko kuma rashin kayayyakin aiki ba, sannan kuma siyasa ba ta taka rawa wajen daukan matakin ba a kurarren lokaci.

Farfesan ya ce, sun dauki matakin dage zaben ne a hukumance bayan wata ganawa da ta gudana a tsakanin jami’an hukumar ta INEC a cikin daren da ya gabata.

Sai dai a cewarsa, matsalar isar da kayayyaki zabe da kuma gobarar da ta tashi a wasu ofisoshin INEC na cikin dalilan dage zaben.

Ana ci gaba da cece-kuce kan batun dage zaben na Najeriya da aka shirya gudanarwa a yau Asabar, in da hatta manyan ‘yan takarar jam’iyyun APC da PDP, wato Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar suka bayyana rashin jin dadinsu.

‘Yan Najeriya da masharhanta sun yi ta tsokaci mabanbanta kan dage zaben wanda ake sa ran kimanin mutane miliyan 84 za su kada kuri’a.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment