Sunday, 10 February 2019

Ba Za A Yi Zabe A Zamfara Ba Matukar Aka Cire APC>>Gwamna Yari Ya Gargadi INEC

Gwamnan jihar Zamfara, Abdul'Aziz Yari Abubakar, ya yi barazanar cewa ba za a gabatar da wani zabe a jihar ba matukar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta cire 'yan takarkarun jam'iyar APC a zabukan da ke gabatowa. 


Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamnan ya yi wannan jawabin yayin kamfe din da jam'iyar tasu ta APC ta gabatar a karamar hukumar Talata Mafara, jihar Zamfara.
Sarauniya.


No comments:

Post a Comment