Tuesday, 12 February 2019

"Babu Dan Takarar Da Darikar Tijjaniyya Ta Umarci Mabiyanta Su Zaba A Matsayin Shugaban Kasa"

Daga Shugaban Majalisar Malamai Na Kungiyar Fityanul Islam Reshen Babban Birnin Tarayya Abuja Imam Murabbi Cisse Alyarwawy.

Tarikarmu Ta Tijjaniyya Ba Kungiya ba ce, Hanya ce Da Bawa Yake Binta Don Ta Kai shi Ga Samun Yardar Ubangiji Ba Samun Abin Duniya Ba.


Kuma Tijjaniyya Ba ta Da Wani Dan Takara Da Ta Tsayar Ko Ta yi Nuni A Zabe shi A Matsayin Shugaban kasa Ko Wani Abu.

Sai Dai Mu Ya'yanta Kowa Daga Cikin mu Yana da Gwaninsa Da Zai Zaba Ko A Matsayin Shugaban kasa Ko A Matsayin Gwamna Ko Sanata Da Sauransu.

Wasun mu Suna da Ra'ayin Zabar 'Yan Takarkaru Daga Jam'iyyar APC, Wasun mu Kuma Suna da Ra'ayin Zabar 'Yan Takarkaru Daga Jam'iyyar PDP. Babu Shakka Dukkannin Jagororimmu Na Tarika Suna Kan Wannan Bayanin nawa.

 Don Haka Ya kamata 'Yan Uwana Tijjanawa Mu ji Tsoron Allah Mu daina Yada Karerayi Sabanin Abinda Muke Kai Don Kawai Neman Abin Duniya Mai karewa.

 Kawai Daga Mutum Ya Assasa Wata Kungiya Ya yi mata Rajista A Gwamnati Sai Ya kama Maula Da Ita Yace Wai Yana Magana ne Da Yawun Dukkannin 'Yan Tijjaniyya Kamar Yadda Su Tamasini Ahmad Rufa'i Okene Suka yi.

Mu Ba Makiya Shugaba Buhari Bane Hasali ma Ni Mai Wannan Maganar InshaAllahu Shi Zan Kadawa Kuri'ta Amma Wannan Dabi'ar da Wasu Daga Cikin mu Suka Dauka Ba Tamu Bace, Ta 'Yan Kungiya ce Kuma Ko Wanne Tsuntsu Kukan Gidansu Yake Yi.

Allah Ka sanya Abinda Muke So Cikin Abinda Kake So Ka Sanya Zabin mu Cikin Zabin ka Albarkar Maulana Rasulullahi S.A.W.


No comments:

Post a Comment