Saturday, 9 February 2019

Babu Inda Na Taba Furta Cewa "Iya Yawan Kuri'un 'Yan Izala Ya Ishi Buhari Ya Ci Zabe, Don Haka Ba Ma Bukatar Kuri'un 'Yan Darika>>Sheik Kabiru Gombe

Babu Inda Na Taba Furta Cewa "Iya Yawan Kuri'un 'Yan Izala Ya Ishi Buhari Ya Ci Zabe, Don Haka Ba Ma Bukatar Kuri'un 'Yan Darika, Cewar Sheik Kabiru Gombe


Shahararren Malamin nan Sheikh Kabiru Gombe yace bai taba furta cewa "Iya Yawan Kuri'un 'Yan Izala Ya Ishi Buhari Ya Ci Zabe ba, Don Haka Ba Ma Bukatar Kuri'un 'Yan Darika" Shehin Malamin yace wannan karya ce da kirkiran Labarin karya irin na 'Yan shi'a. 

"Duk wa'azin da IZALA take gabatarwa akwai kaset na wa'azin, dan haka mun Kalubalanci wadanda suka kirkiri labarin dasu saka Murya ko Video na inda muka fadi haka, in kuma basu kawo ba zaku gane cewa zunzurutun makaryata ne "Inji Shi"

Kazalika ana kara jan hankalin mutane da su kara lura tunda zabe ya kusa zuwa, makiya sun dinga kirkirar labaran karya suna yadawa akan Malaman Sunnah, saboda kiyayyar su da Sunnah, da kuma shugaba Buhari, amma ta Allah ba ta su ba. 

Su wadannan makaryata, idan sun je wajen Kiristoci ce musu suke yi wai Buhari zai musuluntar da Nijeriya. 

Dan haka Shehin Malamin ya nemi jama'a da su yi watsi da wannan zancen, kuma yace IZALA tana nan akan matsayarta na zaben shugaban kasa ranar Asabar a futo a zabi Muhamnadu Buhari.
Rariya.


No comments:

Post a Comment