Sunday, 17 February 2019

Barcelona ta yiwa Real Villadoli ci daya me ban haushi: Messi ya barar da Fenareti ya kuma kafa tarihi

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta yiwa abokiyar karawarta, Real Valladolid ci daya me ban haushi a wasan da suka buga yau, Messi ne ya ciwa Barca kwallon ta hanyar bugun daga kai sai gola tin kamin akai ga zuwa hutun rabin lokaci.
Wannan kwallon da yaci ce ta zamo ta 30 da ya ciwa Barca a kakar wasan 2018/19 kuma hakan yasa ya kafa tarihin ciwa Barcan kwallaye sama da 30 a kowace kakar wasa da ya bugawa Barca wasanni cikin kakannin wasanni 11 da ya shafe a kungiyar.

Messi ya sake samun bugun daga kai sai Gola bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci amma ya barar da damar, masu sharhi sunce 'yan wasan Barca basu taka rawar gani ba a wasan na daren yau.

No comments:

Post a Comment