Tuesday, 19 February 2019

Buhari be da kudin da zan sata kuma nafi jihar Osun kudi>>Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari bashi da kudin da zai sata ko kuma zasu rudashi haka kuma ya bayyana cewa yafi jihar Osun kudi.A kwanakin baya an ruwaito Tunibu na cewa ya fi jihar Osun kudi amma masu taimakamai akan harkar sadarwa suka karyata wannan batu, saidai a yanzu Tinubun ya fito da kanshi ya tabbatar da wannan labari, kamar yanda Punch ta ruwaito.

Tinubu yace ba dan kudi yake tare da Buhari ba dan Buharin beda kudin da zai sata, shiyasa duk alkawarin da yayiwa Buharin yana yinshine da gaske, kuri'un da zai ba Buhari a cikin aljihunshine zai cire kudi ya biya, dan Buharin be da kudin da zai sayi kuri'ar Legas.

Tinubu ya kara da cewa, ya fadi cewa yafi jihar Osun kudi amma be san ana nadar muryarshiba, ya kara da cewa dik wanda ya kawo mai nasara a mazabarshi zai bashi kudi na mamaki amma ba zai ba mutum kudi ba kamin ya mai aiki ba irin na zabukan baya ba, sai ya ga sakamako sannan zai biya.

No comments:

Post a Comment