Saturday, 9 February 2019

Buhari ya hana wa Atiku wurin taro a Abuja>>PDP

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta zargi Buhari da jam'iyyarsa ta APC da hana wa dan takararta Atiku Abubakar filin taron yakin neman zabensa a Abuja.


Wata sanarwa da kakakin jam'iyyar Kola Ologbondiyan ya raba wa manema labarai, ta ce an hana su filin taro na Old Parade Ground a birnin Abuja, duk da sun riga sun biya kuma sun samu izinin amfani da filin taron.

PDP ta shirya gudanar gangamin siyasar ne a ranar Asabar a ci gaba da yakin neman zaben dan takararta Alhaji Atiku Abubakar.

Zuwa yanzu babu martani da ya fito daga fadar shugaban kasa ko daga jam'iyyar APC mai mulki kan dalilin hana wa dan takarar na PDP gudanar da gangamin yakin neman zabensa a Abuja.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment