Monday, 18 February 2019

Bukola Saraki ya fi kowa bayar da gudummuwar kudi lokacin yakin neman zaben Buhari>>Doyin Okupe

Tsohon me taimakawa shugaban kasa shawara akan harkar watsa labarai kuma me baiwa shugaban yakin neman zaben PDP, Sanata Bukola Saraki shawara, Doyin Okupe ya bayyana yanda ministan watsa labarai Lai Muhammad ya ci amanar Sarakin.A jawabin da yayi, kamar yanda jaridar Punch ta ruwaito Doyin Okupe ya bayyana cewa kaf cikin wanda suka bayar da gudummuwar kudi a lokacin yakin neman zaben Buhari a 2015 babu wanda yakai Saraki bayar da kudi masu tsoka, ya bayar da gudummuwa fiye da ta Bola Tinubu da Amaechi.

Ya kara da cewa a wancan lokacin an zauna aka yi alkawarin cewa idan aka kafa gwamnati za'a baiwa Saraki mukamin kakakin majalisar dattijai da kuma damar kawo ministoci biyu.

Bayan kafa gwamnati ne sai shugaba Buhari ya kira Saraki ya gayamai cewa ba zai samu minista biyu da aka mai alkawari ba saidai guda daya, a haka Sarakin ya hakura. Bayan gwana biyu sai shugaban kasar ya sake kiranshi yace guda dayan ma bazai samu ba yana rokonshi alfarmar ya hakura a baiwa Lai Muhammad Ministan watsa labarai.

Anan Saraki yacewa shugaba Buhari me zai hana ya roki Tinubu shima ya hakura da minista daya, sai Buharin ya gayamai cewa, yayi- yayi da Tinubun amma yaki yadda.

Nan saraki yace to kamin ya amince zai koma jiharsu inda shi da Lai Muhammad din suka fito, Kwara dan ya tattauna batun da magoya bayanshi.

Doyin ya kara da cewa da kyar jigogin siyasar Kwara suka yadda aka barwa Lai Muhammad matsayin ministan, sun kuma kirashi suka tattauna dashi, Doyin yace Lai Muhammad yayi ta kuka yana birgima a kasa da rantse-rantse da roko. Jiga-jigan jam'iyyar sun gayawa Lai cewa ba danshi zasu amince ba dan basu yadda dashi ba, zasu amincene kawai saboda kimar shugaban kasa, Muhammadu Buhari da suke gani da kuma dan Allah.

Doyin ya kara da cewa, amma gashi wai yau Lai Muhammad ne gaba-gaba wajan ganin an tumbuke Saraki daga mukaminshi.

No comments:

Post a Comment