Tuesday, 12 February 2019

Cavani ba zai buga karawa da United ba

Watakila Edison Cavani ba zai buga wa Paris St-Germain gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League da Manchester United ba.


Dan wasan mai shekara 31 ya yi rauni ne a bayan da ya ci fenariti a fafatawar da Paris St-Germain ta yi nasarar doke Bordeau 1-0 a ranar Asabar.

Haka shi kuwa dan wasan Brazil, Neymar ba zai buga fafatawar gida da waje da PSG da United za su yi ba, sakamakon jinya da ya ke yi.


Neymar ya yi rauni ne a ranar 23 ga watan Janairu a wasan da PSG ta doke Strasbourg a Kofin FA, bayan da likitoci suka duba shi ne suka sanar da zai yi jinyar mako 10.

Kawo yanzu Kylian Mbappe ne ke koshin lafiya cikin 'yan wasan gaba da ke ci wa PSG kwallaye a fitattun da take da su.

PSG za ta ziyarci Old Trafford domin buga wasan farko a ranar Talata 12 ga watan Fabrairu, sannan su buga wasa na biyu a ranar 6 ga watan Maris a Faransa.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment