Tuesday, 12 February 2019

Champions League: Man United da PSG

Manchester United za ta karbi bakuncin Paris Saint-Germain a wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarun Turai da za su kara a Old Trafford a ranar Talata.


Wannan ne karon farko da kungiyoyin za su fafata a babbar gasa musamman ta zakarun Turai ta Champions League.

Jose Mourinho ne ya kai United zagaye na biyu a gasar ta Champions League ta bana, daga baya ta kore shi a cikin watan Disamba ta nada kocin rikon kwarya Ole Gunnar Solskjaer.


Solskjaer ya ja ragamar United wasa 11, ya kuma ci 10 da canjaras daya, tun bayan da ya maye gurbin Mourinho.

Rabon da United ta kai karawar daf da na kusa da na karshe tun kakar 2014, ita kuwa PSG tun 2016 rabon da ta kai matakin.

Dan wasan PSG, Neymar da kuma Meunier ba za su buga karawar ba, sakamakon jinya da suke yi, haka kuma da kyar ne idan Edison Cavani zai buga wa kungiyar Faransa fafatawar.

Manchester United tana da kofin Zakarun Turai uku, ita kuwa PSG ba ta taba dauka ba.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment