Friday, 15 February 2019

Da gangan malaman Izala suka juya kalaman kwankwaso don a tasaneshi>>Sheikh Aminu Daurawa

Sai dai kuma a wani abu da ya yi kama da gaskata maganar Kwankwaso, Sheikh Daurawa ya jagoranci limamai sama da dari zuwa gidan Kwankwaso don su jaddada goyon bayansu ga shi Kwankwason.


Daurawa ya bayyana cewa da gangan Malaman Izala suka juya kalaman Kwankwaso don su harzuka magoyaba bayansu su tsani Kwankwaso.

Daurawa ya kara da cewa, Kwankwaso bai yi wani kuskure ba a kalamansa na cewa wasu malamai na fakewa da gemu su aikata sabo da goyon bayan cin hanci da rashawa da kama karya.

Ya ci gaba da cewa, da a ce Kwankwaso makiyin addinin musulunci ne da bai kaddamar da shari’ar musulunci a Kano ba, da kuma bai kafa Hisba ba, da kuma bai gina azuzuwa a makarantun Islamiyya ba da kuma bai aurar da zaurawa ba.

Wasu manyan malamai daga cikin wadanda suka yi wa Daurawa rakiya sun hada da: Sheikh Sani Ashir, Sheikh Malam Nazifi, Sheikh Abubakar Kandahar da Sheikh Gwani Sanusi.

Sauran sun hada da: Sheikh Alkali Mustapha, Sheikh Bazallah Kabara, Sheikh Buba Jada, Sheikh Isma’ila Mangu, Shiekh Malam Kabiru da dai sauransu.
Sarauniya.


No comments:

Post a Comment