Monday, 18 February 2019

Dage Zabe: Dalilin da kuka bayar na rashin kyawun yanayi ba gaskiyabane>>Ministan Buhari ya gayawa INEC

Ministan sufuri, Hadi Sirika ya karyata ikirarin hukumar zabe me zaman kanta INEC na cewa da ta yi daya daga cikin matsalolin da ta samu da suka sa ta dage zabe hadda matsalar rashin kyawun yanayi da aka samu.A cikin wani sako da ya fitar ta dandalinshi na sada zumuntar Twitter,Hadi Sirika ya bayyana cewa, INEC ta samu wani dalilin da ya hanata yin zabe amma maganar rashin kyawun yanayi a lokutan zabe ba, ba gaskiya bane, asalima babu wannan matsalar kuma an baiwa tashoshin jiragen sama izinin yin aiki awanni 24 a lokacin zaben.

INEC dai ta bayar da matsalar rashin kyawun yanayi ne wanda tace yana daga cikin abinda yasa kayan aikinta basu isa guraren da ya kamata da wuri ba.

Saidai duk da waccan sanarwar ta Hadi Sirika INEC ta nace akan cewa, akwai matsalar rashin kyawun yana, wani ma'aikacin INEC din ya bayyanawa maneman labarai cewa, ai ba su ce wai an samu matsalar tashin kyawun yanayi a ranekun Asabar ko Juma'a ba.

No comments:

Post a Comment