Saturday, 16 February 2019

Dama can INEC bata shirya yin zabe ba>>Balabe Musa

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Balarabe Musa ya bayyana cewa be ji dadin daga zaben da hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta yi ba amma abin be bashi mamaki ba saboda matsalolin na INEC a bayyane suke.Da yake hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN Balarabe Musa yace a bayyane yake INEC na da matsalar kudi domin kudun da majalisar tarayya ta amince mata wajan aikin zabe ba zasu isheta ba kuma babu tabbas ma idan gwamnatin tarayya ta bata kudin gaba daya.

Ya kara da cewa akwai kuma matsalar tsaro da ake fama da ita ta yanda su kansu INEC din abin ya shafesu.

Ya ce fatanshi shine masu ruwa da tsaki a harkar zaben zasu baiwa INEC din hadin kai dan samun shawo kan matsalolin da take fuskanta.

Balarabe Musa ya karkare da cewa 'yan Najeriya su yi hakuri su kara shiri kamin zuwan sabon lokacin zaben da INEC ta saka.

No comments:

Post a Comment